Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami gawar dan jaridar da ya bace a jihar Michoacan


Mexico Journalist Killed
Mexico Journalist Killed

Salvador Adame, darektan wata tashar talabijin a kasar 6TV, an sace shi ne ranar goma sha takwas ga watan Mayu a birnin Nueva, Italia, dake tazarar kilomita dari hudu daga birnin Mexico.

Jami’an jihar sun fada jiya Litinin cewa, an sami gawar Adame da aka kona, a tsakiyar watan Yuni, aka kuma tantanceta ta wajen gwajin kwayar halitta.

An sace Adame ne bayanda aka fito da wani fitaccen dan jarida Javier Valdez daga motarsa aka kashe shi da tsakar rana a Culiacan, jihar Sinaloa ta kasar Mexico.

Kwamitin kare rayukan ‘yan jarida mai shelkwata a birnin NY, yace an kashe ‘yan jarida arba’in a Mexico bisa dalilan da aka tantance suna da alaka da ayyukansu tun daga shekara ta dubu da dari tara da casa’in da biyu, an kuma kashe wadansu hamsin a lokacin karkashin wadansu yanayi da ba a tantance ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG