Accessibility links

An sami kananan yara 45 dauke da kwayar cutar shan inna bana a Najeriya


Wadansu 'yan yara

Kananan yara 45 aka samu dauke da kwayar cutar shan inna a jihohi goma na Najeriya

Kananan yara 45 aka samu dauke da kwayar cutar shan inna a jihohi goma na Najeriya, tsakanin watan Janairu zuwa Yunin wannan shekarar, akasin 25 da aka samu a daidai wannan lokacin bara.

Asusun tallafi na kananan yara UNICEF ne ya bayyanan haka a cikin wani rahoto da ya bayar. Bisa ga rahoton, kowanne yaro daya cikin uku a jihohin Borno da Kano da Sokoto da kuma Yobe inda aka fi samun yara dauke da kwayar cutar, basu sami maganin rigakafi sau hudu ba, yayinda aka sake samun bullar cutar a jihohin Kaduna da Niger cikin shekara ta dubu biyu da goma sha biyu bayan shafe shekaru ba tare da an sami ko yaro daya dauke da kwayar cutar ba.

Rahoton ya kuma nuna cewa, an sami raguwar yaran da ba a samu a gida lokacin gudanar da rigakafin, yayinda ake rasa samun kananan yara da dama lokacin gudanar da allurar rigakafi a Najeriya.

Bisa ga rahoton na UNICEF ana ci gaba da samun ingancin aikin rigakafi idan aka kwatanta da shekarun baya.

Kididdiga ta baya bayan nan na nuni da cewa, Kano tafi kowacce jiha yawan kananan yaran da ba a yiwa allurar rigakafi ba, biye da Kebbi da kuma Sokoto.

Rashin bada hadin kai da iyaye ke yi, yana daya daga cikin dalilan da suka sa aka gaza yiwa kimanin kashi 24 na kananan yara rigakafi a lokacin rigakafin da aka gudanar cikin watan Mayu.

Ta dalilin haka, asusun UNICEF, tare da hadin guiwar shirin kiwon lafiya matakin farko na kasa, suka tura tawagar ma’aikatan sa kai masu tada tsimin jama’a da nufin shawo kan wannan matsalar. Inda ake kyautata zaton tura kimanin ma’aikatan sa kai dubu biyu da dari da hamsin a wuraren da aka hana yiwa kananan yara rigakafi.

XS
SM
MD
LG