Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Karuwar 'Yan Gudun Hijira A Najeriya


'Yan gudun hijira sandiyar hare-haren 'yan Boko Haram sun karban kayayyakin agaji da suka hada da abinci a sansanin 'yan gudun hijira a Yola.

Mutanen dake zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira aciki da wajen Abuja da kan dogara kan tallafi na hukumomi da ‘dai ‘dai kun jama’a.

‘Yan gudun hijirar dai nada ra’ayi daya, na fatan lamura su daidai ta a garuruwansu, domin su koma gida.

A sakamakon rikice rikicen kabilanci, da gaba tsakanin manoma da makiyaya, zuwa mafi muni rashin tsaro daga hare-haren ta’addancin ‘yan kungiyar Boko Haram, ya sanya ‘yan gudun hijira a Najeriya dake cikin gida da wanda suka tsallake, ya haura dubu dari bakwai.

Tabakin kwamishinar kula da ‘yan gudun hijira ta Najeriya, Hadiza Sani Kan Giwa tace, “a kwai mata da yara da suka rasa mazajensu da iyayensu, akwai maza da suka rasa matsugunni suka rasa sana’a, wasu kuma basu da lafiya, gwamnatin tarayya tana iyakacin kokarinta, banda hukumarmu, akwai hukumomi dayawa, akwai hukuma kamar NEMA, kuma kusan kowacce hukuma ta gwamnatin tarayya, tana iyakacin kokari taga cewa anshawo kan wannan al’amari, to amma ance in danbu yayi yawa ance bayajin mai.”

Rashin tsaro a yankuna da dama na Najeriya, na matukar illa ga ilimi, harkokin kiwon lafiya da tattalin arziki.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG