Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami koma bayan kan harkokin tsaro a yankin Darfur na Sudan


Mutanen da suka rasa muhallinsu ne ke jiran a soma raba musu kayan agaji a garin Akobo dake kudancin Sudan. (file)
Mutanen da suka rasa muhallinsu ne ke jiran a soma raba musu kayan agaji a garin Akobo dake kudancin Sudan. (file)

Duk da shawarwari da ake yi tskanin Sudan da wata babbar kungiyar ‘yan tawaye daga yankin Darfur, harkokin tsaro sun tabarbare a yankin, inji Jakada Gambari.

Shugaban ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Darfur, ya ce an sami tabarbarewar harkokin tsaro a yankin duk da shawarwari da ake yi tsakanin gwamnatin kasar da daya daga cikin manyan kungiyoyin ‘yan tawaye dake yankin.

Ranar Talata ce Ibrahim Gambari, ya gayawa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, ana samun ci gaba sannu a hankali, a shawarwarin da ake yi tsakanin Sudan da kungiyar ‘yan tawayen LJM ko Liberation and Justice Movement a Qatar. Amma jakada Gambari ya ce “babban abin bakin ciki ne” ganin wakilan wasu kungiyoyin ‘yan tawaye biyu basu shiga shawarwarin ba. An kammala zagaye shawarwari na baya bayan cikin wan nan wata.

Kungiyoyin ‘yan tawayen da basu shiga shawarwarin ba sun hada da SLA da JEM, wadan da suka janye daga shawarwarin cikin watan Mayu suka koma fagen daga. Darfur tana fama da yaki tun 2003, lokacin da ‘yan tawaye suka dauki makamai, suna zargin gwamnatin kasar da yin watsi da yankin.

Jakadiyar Amurka a MDD Susan Rice, ta ce lamarin na Darfur abin tada da hankali ne. Gambari ya ce lamarin a Darfur ya kara tabarbarewa tun bayan rahoton da ya gabatar cikin watan jiya,lokacin ya kira lamarin da cewa “mummuna”.

XS
SM
MD
LG