Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Tsohon Frai Ministan Faransa Da Cin Hanci


Francois Fillon, tsohon frai ministan Faransa

Wata kotu a birnin Paris na kasar Faransa ta kama tsohon Fraim Ministan Faransa, Francois Fillon da laifi yin amfani da kudaden gwamnati wajen biyan matarsa da yaransa domin aikin da basu yi ba.

Matarsa, Penelope Fillon itama an same ta da laifin taimaka masa. Har yanzu dai kotun ba ta ba da cikakken bayani akan hukuncin ba.

Francois Fillon da matarsa Peneloppe
Francois Fillon da matarsa Peneloppe


Wannan aikin ya samar musu da kudi fiye da Euro miliyan daya tun daga shekarar 1998.

Wannan badakala ta bayyana a kafofin yada labarai watanni uku kafin zaben shugaban kasar a shekarar 2017. Lamarin da ya janyo ya koma daga na daya a yakin, zuwa na uku.

Fillon wanda ya zama fraim ministan Faransa tun daga shekarar 2007 zuwa 2012, da matarsa sun musanta aikata wannan laifin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG