Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Akwatunan Kudi a Gidan Omar Al Bashir a Sudan


Hambararren shugaban Sudan, Omar Al Bashir
Hambararren shugaban Sudan, Omar Al Bashir

Yanzu haka ana kuma tsare da wasu ‘yan uwansa biyu, wadanda su ma za a tuhume su da laifin cin hanci da rashawa, a cewar majiyar.

Wata majiya a ma’aikatar shari’ar kasar Sudan, ta ce masu shigar da kara, sun fara tuhumar hambararren shugaban kasar, Omar Al Bashir da laifukan karkata kudaden kasar da kuma ajiye wasu makudan kudaden kasashen waje ba bisa ka’ida ba.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters, shi ma ya tabbatar da wannan labari.

Majiyar ta ce, sojojin kasar masu tattara bayanan sirri, wadanda suka binciki gidan tsohon shugaban, sun samu akwatuna makare da kudade, da yawansu ya haura dala dubu 351 da kudin euro miliyan shida da kuma pam dan kasar ta Sudan.

Ana sa ran za a yi wa Al Bashir tambayoyi a gidan yarin da ake tsare da shi na Kobar.

Yanzu haka ana kuma tsare da wasu ‘yan uwansa biyu, wadanda su ma za a tuhume su da laifin cin hanci da rashawa, a cewar majiyar.

Yunkurin jin ta bakin wasu daga cikin iyalan tsohon shugaban ya cutura.

An hambarar da gwamnatin Shugaba Omar Al Bashir ne a ranar 11 ga watan Afrilu, wanda har ila yau kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ke nemansa ruwa a jallo domin ya amsa zargin da ake masa na aikata kisan kare dangi a yankin yammacin Dafur.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG