Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Barkewar Cutar Sankarau A Jihohi Uku A Nijar


 Taron cututtuka, ministan kiwon lafiyar Nijar Dr Iliyasu Idi Mai Nasara
Taron cututtuka, ministan kiwon lafiyar Nijar Dr Iliyasu Idi Mai Nasara

Ministan kiwon lafiya a jamhuriyar Nijar ya tabbatar da barkewar cutar sankarau a jihohi uku na kasar tare da bayyana alamun kamuwa da cutar da kuma sanar da jama'a cewa maganin sankarau kyauta ne kuma yana koina a asibitoci da dakunan shan magani .

A hira da yayi da wakilin Sashen Hausa a birnin Yamai, ministan kiwon lafiyar kasar Dr.Iliyasu Idi Mai Nasara, ya tabbatar da barkewar cutar a jihohi uku duk da cewa bai bada adadin wadanda suka kamu da cutar ba.

A cewarsa duk shekara a yankin Afirka akan samu cututka da dama musamman cutar sankarau lokacin zafi. Saboda haka abun da su keyi a hukumance shi ne a fito a yiwa mutane bayani saboda ba sabon abu ba ne.

Injishi da akan samu ciwon ne tun watan Janairu amma wannan shekarar sai da aka shiga watan Afirilu cutar ta kunno kai. Kawo yanzu dai akwai wurare uku zuwa hudu cikin kasar da mutane suka kamu da cutar.

Garuruwan da aka samu bullar cutar sun hada da gari guda a jihar Damagaran da yankin Dan Isa a jihar Maradi, a jihar Tohoua kuma a yankin Bunza.

Ministan ya ce suna fadawa mutane matakin da suka dauka tare da bayyana alamun kamuwa da cutar. Idan mutum babba ne, alamun kamuwa da cutar sun hada da ciwon kai da zafin jiki da amai ko kuma kagewar wuya.Idan kuma yaro ne karami madiga ta kage kuma ya ki shan nono ya dinga kuka.

Ministan ya ce yanzu ba zai iya bada adadin wadanda suka kamu da cutar ba amma ana nan ana tattara alkalumma. An dai tura magani ana kuma jiran sakamako.

Kawo yanzu babu asarar rai amma ana ci gaba da daukan matakai kamar fadakar da mutane tare da jinya kyauta.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG