Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An samu daidaituwa tsakanin 'yansanda da maharba a Adamawa


Maharba da kayan yakinsu a yankin Adamawa
Maharba da kayan yakinsu a yankin Adamawa

Maharban jihar Adamawa suke kula da wuraren da sojoji suka kwato daga hannun 'yan Boko Haram kafin 'yansandan jihar su kama shugabanninsu lamarin da ya sa suka fusata suka kuma janye daga ikin da suke yiwa jiharsu

Maharban sun janye ne daga yankunan da aka kwato daga mayakan Boko Haram saboda takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu da 'yansandan jihar da ta kaiga kama wasunsu.

Sun janye ne domin nuna fushinsu da kamun da rundunar 'yansanda ta yiwa shugaban maharban tare da wasu jami'ansu.

Shugaban maharban a jihar Alhaji Muhammad Tula yace yadda suka rike amana duk membobinsu na ciki da waje su kwantar da hankulansu, su yi hakuri su koma bakin aikinsu. Yace babu abun da zai biyo baya amma hakuri yake bayarwa.

Wani kusa a kungiyar dake kula da shiyar Gombe yace tare 'yansanda suka rikesu. Yace abun da Allah ya kaddara babu mai kawar dashi. Ya godewa jama'a da masu goyon bayansu. Yace Lamidon Adamawa ya kirasu ya ja kunnuwansu. Sun fahimtardasu abubuwan dake tafiya.

Mata ma suna taka rawa akungiyar maharban domin dasu aka fafata da mayakan Boko Haram. Wata cikinsu tace bata ci dadin abun da ya faru ba. Ta ba iyayen kasa hakuri da iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

XS
SM
MD
LG