Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tuhumar Da Ake Yiwa Kwamandan Kungiyar Maharban Dake Yakar Boko Haram


Maharba da Kayan Yakinsu, 14 ga Nuwamba 2014.

An zargi wasu mukarraban kungiyar maharba na jihar Adamawa, da gabatar da shaidun boge a tuhumar da ake wa kwamandanta da yanzu haka ke fuskantar tuhumar sayarwa ‘yan bata gari makamai Mr, Morris Enoch, domin yin rufa-rufa ga ayukan almundahana da zarmiya a kungiyar.

Mr, Andrew Walye tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, shine ya furta hakan ga taron manema labarai a Yola, cewa wanda ake tuhumar a bara ya gabatar da takardar koke ga hukumomin tsaro kan wasu bindigogo da aka kwato daga hanun ‘yan Boko Haram, amma aka karkatasu ba tare an mika su ga hukuma ba wanda har yanzu ba a gudanar da bincike ba.

Bincike da wakilin Muryar Amurka, ya gudanar ya nuna cewa baya ga zargin karkata makamai da ‘ya’yan kungiyar ke yiwa juna, akwai wani batun na rub-da-ciki kan kudin tallafi da gwamnati ke baiwa kungiyar wanda ya sa ta dare biyu - inji Mal. Ephraim Abdullahi.

Da yake amsa tambayar ko gaskiya ne rabon tallafin da gwamnati ke baiwa kungiyar na daga cikin dalilin da suk yi wa juna tonon silili Alhaji Yakubu Ali, ya tabbatar da haka kamar yadda da zaku ji a cikin sauti cikin rahotan da ke kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG