Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Gawa 137 A Cikin Mushen Jirgin Saman DANA

Neman gwarwakin wadanda su ka mutu a cikin hatsarin jirgin saman DANA

Shugaba Jonathan ya yi alkawarin cewa irin wannan bala'i ba zai sake faruwa ba

Tawagogin ma'aikatan neman gawa sun gano gawarwaki dari da talatin da bakwai daga cikin mushen jirgin saman da ya fadi ranar Lahadi a wata unguwar birnin Lagos.

'Yan sanda na tsaye a inda jirgin saman ya fadi
'Yan sanda na tsaye a inda jirgin saman ya fadi

Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana kwanaki uku na makoki da juyayi da alhini. Ya ziyarci inda jirgin saman ya fadi kuma ya yi alkawarin cewa iri wannan bala'i ba zai sake faruwa, kuma ya sha alwashin daukan matakan kyautata hanyoyin kiyaye lafiyar zirga-zirgar jiragen sama.

Duka fasinjojin jirgin da ma'aikatan shi baki daya su dari da hamsin da uku sun mutu tare da wasu mutane a kasa wadanda ba a san adadin su ba.

Jim kadan kafin kafin jirgin saman ya fadi matukin jirgin ya sanar da cewa akwai wata matsalar inji. Amma jami'ai sun ce da sauran lokaci kafin a tabbatar da gaskiyar abun da ya haddasa hatsarin jirgin saman.

'Yan kallo sun taru yayin da 'yan kwana-kwana ke kokarin kashe wutar da ta tashi lokacin da jirgin saman kamfanin Dana Airlines ya fadi a wata unguwar Lagos bayan tasowar shi daga Abuja ranar lahadi 3 Yuni, 2012.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG