Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 22,614.
Adadin ya kai wanann matakin ne bayan da aka samu karin mutum 594 da suka kamu da cutar a jihohi 22.
Jihohin da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Lagas inda aka samu mutum 159, 106 a Delta, 44 a Ondo, 34 a Abuja, 34 a Edo, 33 a Oyo, 33 a Kaduna, 28 a Enugu, 25 a Katsina, 22 a Imo, 15 a Adamawa, 12 a Ogun, 11 a Osun.
Sauran jihohin sun hada da Abia mai mutum 8, 6 a Rivers, 5 a Nasarawa, 5 a Bauchi, 5 a Neja, 4 a Kebbi, 3 a Ekiti sai kuma 1 a Plateau da Taraba.
Jihar Legas dai har yanzu ita ce kan gaba ta fannin masu kamu da COVID-19 a Najeriya, yanzu gaba dayan adadinta ya kai 9,482.
Sanarwar da hukumar ta NCDC ta fidda a shafinta na Twitter ranar Alhamis 25 ga watan Yuni ta kuma ce ya zuwa yanzu an sallami mutum 7,822 daga asibiti kana mutum 549 sun mutu.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 26, 2021
Adadin Dalibai Mata 317 Aka Sace A Zamfara - 'Yan Sanda
-
Fabrairu 27, 2021
Jihohin Zamfara, Kano Sun Rufe Makarantun Kwana
-
Fabrairu 26, 2021
Lokacin Lallashin Masu Daukar Makami Ya Wuce- Buhari
-
Fabrairu 26, 2021
UNICEF Ta Yi Allah Wadai Da Sace ‘Yan Mata A Zamfara
Facebook Forum