Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Karin Mutum 576 Da Suka Kamu Da COVID-19 A Najeriya


Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce cikin sa’o’i 24 an samu karin mutum 576 da suka harbu da COVID-19, kwayar cutar da ke haddasa coronavirus.

Sanarwar da Hukumar NCDC ta fitar a shafinta na Twitter jiya Talata, 21 ga watan Yuli ta ce adadin wadanda aka tabbatar sun kamu a kasar yanzu ya kai 37,801.

Jihohin da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Lagos inda aka samu mutum 88, 87 a Kwara, 82 a Abuja, 62 a Plateau, 39 a Ondo, 28 a Enugu, 26 a Oyo, 24 a Taraba, 20 a Kaduna, 20 a Ebonyi, 17 a Cross River, 14 a Kano.

Sauran jihohin sun hada da mutum 11 a Rivers, 10 a Ogun, 9 a Delta, 8 a Nasarawa, 8 a Osun, 3 a Katsina, 2 a Imo da kuma Kebbi da Borno 1.

Sai dai hukumar NCDC ta ce ya zuwa yanzu an sallami mutum 15,677, kana mutum 805 suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG