Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Maganin Rigakafin Cutar Ebola


Ana auna cutar Ebola

Masu bincike sun bayyana cewa wani maganin gwaji na rigakafin cutar Ebola na aiki kwarai-da-gaske wajen kiyaye mummunar cutar.

Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya yau Juma’a ta bayyana cewa wannan maganin rigakafi na aiki dari bisa dari a gwaje-gwajen da aka gudanar a kasar Guinea. Wata mujallar kiwon lafiya ta kasar Britaniya mai suna Lancet ta bayyana sakamakon farko na binciken da aka gudanar.

Wannan sabon maganin rigakafi ka iya zama magani mafi inganci wajen kashe kwayoyin cutar Ebola, a cewar ministan harkokin wajen kasar Norway, wato daya daga cikin kasashen da suka taka rawa wajen gudanar da gwaje-gwajen.

Annobar cutar Ebola a yammacin Afirka ta kashe a kalla mutane dubu 11, mafi yawancinsu a Liberiya, Guinea da Saliyo.

Ebola na daya daga cikin cututuka mafi hadari a duniya, dake jawo zazzabi mai zafi. Fatan da ake yi shine na gani wannan sabon maganin riga-kafi shine gagarumin cigaba da aka samu wajen yaki da cutar ta Ebola.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG