Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Yi Bayani Kan Samun Wani Da Coronavirus A Najeriya


Gwamnatin tarayyar Najeriya ta babbatar da samun wani mutum dauke da kwayar cutar Coronavirus a Najeriya.

A wata sanarwa da Ministan Lafiyan Najeriya Dr. Osagie Ehanire ya fitar a
ranar juma’ar nan, yace wani dan kasar Italiya daya fito daga birnin Milan kuma dake aiki a Najeriya ne ya shigo da cutar coronavirus cikin kasar..

An tabbatar da kwayar cutar ne a dakin gwaje-gwaje na jami'ar Lagos, yayin da a ake ci gaba da baiwa mutumin dake dauke da cutar kyakyawar kulawa ta musamman a asibitin Cibiyar Kula Da Yaduwar Cuttutuka dake Yaba a Lagos.

Sai dai kuma ma'aikatar ta sakaya sunan mutumin, da kuma inda aka fara gano alamun cutar a tattare da shi, da kuma wuraren da ya bi kafin a gano cewa yana dauke da cutar.

Ministan Lafiya na Najeriya, Mr. Osagie Ehanire, ya bada sanarwar cewa gwamnati na daukan matakan magance yaduwar cutar a kasar da kuma matakin daukar bular ta a ko da yaushe.

Sanarwar tace, an dauki matakan yaki da cutar ta Coronavirus, karkashin jagorancin Cibiyar Kula Da Yaduwar Cututtuka ta Najeriya NCDC, wacce zata yi aiki tare da asibitin dake Lagos domin tsayar da cutar.

Wani likita a Najeriya, Dr. sadiq Aliyu Hussaini likita a Najeriya wanda kuma yayi karin haske game da matakan rigakafin wannan cutar murar coronavirus. Ya ce da farko mutane su dinga wanke hannuwan su akai akai, da ruwan famfo mai kyau, su yi amfani da abin tsaftace hannu wato sanitizer, kuma kada su taba fuska ko idanunsu.

Tuni dai wannan labari ya fara firgita wasu mazauna birnin na Legas, inda yanzu haka mazauna birnin dama Najeriya ke ci gaba da tattaunawa akan wannan cuta.

Ita ma a sanarwar da ta fitar gwamnatin jihar legas ta hannun kwamishinan
ta na Lafiya Farfesa Akin Abayomi ta shawarci al’ummar jihar su kasance
masu daukan matakan riga kafi na wanke hannuwa da sabulu, da ruwa mai
kyau, yin nesa da jama’a, musanman masu mura. Haka kuma gwamnati ta bada lambobin waya da za’a kira domin sanarwa hukumomi duk wata alamar cutar.

Bugu da kari gwamnati ta gargadi masu anfani da kafofin sadarwan zamani da su guji baza jita jitar kamuwar da cutar, inda gwamnati tace za’a dauki mataki akan duk wani mai yada jita jita.

Birnin Legas dai shi ne birni mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka, don haka gwamnati da hukumomin lafiya suka tashi tsaye. Hukumar Red Cross a Najeriya tace ta shirya tare da 'yan sa kai kimanin dubu 80, kamar yarda wata sanarwa da shugabar kungiyar Mrs. Adebola Kolawale ta gabatar ga 'yan jarida.

Tuni dai cutar lassa ta kashe mutane fiye da 110 a jihohi daban daban na Najeriya.

A saurari cikakken rahoto daga Abuja a Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG