Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Raguwar Cutar Polio da Kashi 67 Cikin 100 A Shekara Guda


Taron yaki da cutar Polio a Jihar Bauchi
Taron yaki da cutar Polio a Jihar Bauchi

Za a bullo da sabbin dabarun bunkasa rigakafi, yayin da aka shafe watanni 6 cur ba a samu ko yaro guda da jinsin kwayar cutar Polio da ake kira Type3 ba

Najeriya ta fadawa kasashen duniya da suka halarci taron majalisar kiwon lafiya ta duniya cewa ta samu nasarar rage yawan masu kamuwa da kwayar cutar shan inna ta Polio da kashi 67 cikin 100, inda zuwa wannan lokaci a shekarar da ta shige aka samu yara 48, yayin da a bana aka samu guda 22 kawai.

Babban darektan Hukumar Kiwon Lafiya Matakin farko ta Najeriya, Dr. Ado Gana Muhammad, ya fadawa taron cewa rabon da a samu wani dauke da jinsin kwayar cutar Polio da ake kira Type3 tun watan nuwambar shekarar da ta shige. Haka kuma yace yawan jinsunan kwayar cutar da ake gani sun ragu daga 14 sun komo 2 kawai.

Dr. Muhammad ya bukaci majalisar da ta fito da sabbin hanyoyi da fasahar rigakafin da kowa zai iya aiwatar da shi ba sai kwararru ba kawai domin a samu kaiwa ga karin yara.
Yace najeriya tana son gaggauta yin amfani da sabbin magungunan rigakafi, sai dai ya lura da cewa sabbin allurai na rigakafi, bisa al’ada, sun fi tsada.

Sai dai kuma Dr. Muhammad yace har yanzu akwai kalubale a gaban kasar nan, musamman a fannin tsaro, a wasu kananan hukumomi 10 a Jihar borno da kuma a Jihar Yobe, inda aka kafa dokar-ta-baci. Yace gwamnati ta kirkiro da sabbin dabarun yaki da cutar a arewa, musamman a yankin arewa maso gabas.
XS
SM
MD
LG