Accessibility links

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Roki A Yi Na'am Da Rigakafin Polio


Taron yaki Da Cutar Polio a Najeriya

Shahararren malamin yace ya zamo wajibi jama'a su yi na'am da rigakafin cutar ta Polio ganin yadda aka samu kawar da agana da ciwon barci.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya roki iyaye da su kyale a yi ma 'ya'yansu rigakafin cutar polio, yana mai fadin cewa an ga amfanin irin wannan yunkurin a can baya, lokacin da aka samu nasarar kawar da cututtuka irinsu agana daga bangon duniya.

Sheikh Dahiru yace ya kamata jama'a su kauda duk wani tunanin da suke yi na zarge-zarge marasa tushe game da wannan yunkurin kawar da cutar Polio, su bayar da 'ya'yansu a diga musu maganin rigakafin wannan cuta.

Shaihin malamin ya ruwaito wani hadisi na Manzon Allah (saw) dake cewa, "rigakafi ya fi magani. Idan cuta yana da rigakafi, gara ka yi shi a kan ciwon ya same ka, ka je neman magani."

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG