Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Raguwar Cutar Shan Inna a Duniya


Ana Bada Maganin Polio
Ana Bada Maganin Polio

Masana kimiya sun yi kashedi a kan gangamin yaki da cutar shan inna a Afrika ta tsakiya cewar yana samun cikas, sakamakon rikici a yankin tabkin kogin Chadi inda har iyau Boko Haram ke gudanar da ayyukanta. A wani albishir kuma an ayyana Gabon kasa mara shan inna.

Shugaban hukumar yaki da cutar shan inna reshen Afrika, Farfesa Rose Leke tace Afrika ta tsakiya bata samu cutar shan inna ba a cikin watanni goma sha biyar da suka wuce. Sai dai ta kara da cewar, masana kimiya ba zasu iya tabbatar da an kawar da kwayar cutar a yankin ba.

Leke tace rukunonin ma’aikatar kiwon lafiya basu samun daman shiga wuraren da ake yaki a Mali, Afrika ta tsakiya, Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo da wasu bangarorin kasar Kamaru, sai kuma Chadi da Nijer da kuma Najeriya wurare da suka sha fama da ta’addancin Boko Haram.

Tace Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo na yada nau’in kwayoyin shan inna da dama. Muna nuna damuwa da wannan kasar, a don haka muna da shawarwari na musamman ga DR Congo da sauran kasashen. Har iyau muna damuwa ga halin da ake ciki a tabkin kogin Chadi da jihar Borno inda bamu san abin dake faruwa a wurin ba. Tace ina ganin wannan dumawa ce ga duniya baki daya.

Rose tace yawan masu kamuwa da cutar shan inna ya ragu da fiye kashi 99 cikin dari cikin shekaru 30 da suka shige, daga akalla dubu dari uku da hamsin a duk shekara zuwa ga 37 kacal a shekarar 2016.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG