Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Wanda Yayi Niyyar Kashe Mandela Da Laifi


Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Nelson Mandela

A bayan makarkashiyar kashe Mandela, an ce Mike Du Toit ya kuma kulla makarkashiyar korar bakaken fata daga Afirka ta Kudu zuwa makwabta

An samu madugun wata makarkashiyar da aka kulla ta kashe Nelson Mandela da korar bakaken fata daga Afirka ta Kudu a shekarar 2002, da laifin cin amanar kasa.

Alhamis ne babbar kotun lardin Gauteng ta Arewa ta samu tsohon malamin jami'a, kuma shugaban wata kungiyar sojojin sa kai da ake kira Boeremag, Mike du Toit, da wannan laifin.

Kungiyar sojojin sa kai da ya jagoranta, ta goyi bayan tsarin mulkin wariyar launin fata, wadda a karkashinsa Turawa 'yan tsiraru suka kanainaye mulki, aka kuma mayarda bakaken fata kamar bayi.

Shaidu sun ce du Toit da magoya bayansa sun tattauna kashe Mandela, bakar fata na farko da ya zamo shugaban Afirka ta Kudu. Haka kuma, sun kitsa wata makarkashiya ta yadda zasu kori bakaken fata zuwa arewacin kasar su ingiza su cikin kasashe makwabta ta yin amfani da abinci a zaman tarko.

Ba a saka ranar da za a bayyana hukumcinsa ba. Nan da 'yan makonni kadan ake sa ran jin sakamakon shari'ar wasu mutanen su fiye da 20 wadanda su ma aka tuhuma da laifin cin amanar kasa. Dukkansu zasu iya fuskantar hukumcin daurin rai da rai.

Shaidu sun fada a shari'ar shekaru 9 da aka gudanar cewa kungiyar sojojin sa kai ta Boeremag ta kai hare-haren bam sau da dama a garin bakar fata mai suna Soweto har mutum guda ya mutu.

Haka kuma, alkali Eben Jordaan yace shaida ta nuna cewa Du Toit shi ne ya wallafa wani kundin ayyana yaki da ake kira "Document 12" wanda aka samu a cikin kwamfutarsa a bayan da 'yan sanda suka kai sumame gidansa a shekarar 2001. Masu gabatar da kara suka ce wannan kundi ya kunshi wani shiri na yadda za a maye gurbin gwamnatin jam'iyyar ANC da gwamnatin soja ta turawa jinsin Afrikaner.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG