Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Samu Wata Fashewa a New York


'Yan sanda sun datse wata hanya a kusa da inda aka samu fashewa a birnin New York

An samu wata fashewa a birnin New York da ke Amurka, kuma hukumomi sun ce har an cafke mutum guda da ake zargi da hanu.

‘Yan sandan birnin New York sun ce a yau Litinin suna tsare da wani mutum, bayan wata fashewa da aka samu a wurin jiran motar fasinja da ke gefen ginin hukumar kula da tashohin ruwa.

‘Yan sandan, sun tabbatar da cewa, wanda ake tsaren da shi na miji ne, wanda shi kadai ya ji rauni a wurin fashewar.

Sai dai hukumomi ba su ba da tabbacin wane irin “abu” aka yi amfani da shi wajen aukuwar wannan lamari ba.

Rahotannin farko sun yi nuni da cewa, fashewar ta auku ne bayan da wani bututu ya fashe.

Tuni dai aka dakatar da zirga zirgar layukan jiragen kasa uku da ke safara a yankin.

Sannan wasu layukan jiragen sun karkata akalar tafiyarsu daga titin da ake kira 42nd Street, wanda ke tsakiyar yankin dandalin Time Square da ke Manhattan, wanda wuri ne da masu yawon bude ke yawan ziyarta.

Sakatariyar yada labarai a Fadar White House, Sarah Huckabee Sanders, ta aike da sako a shafin Twitter, inda ta ce an sanar da Shugaba Donald Trump kan wannan fashewa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG