Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sassauta Dokar Kulle a Kaduna


Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai
Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya gabatar da wani jawabi inda ya sanar cewa za a sassauta dokar takaita zirga-zirga wacce aka yi kwannaki 75 ana fama da ita a jihar.

Gwamnan ya fara da jajantawa 'yan jihar bisa irin kokarin da ya ce sun yi na zama a gida duk da wahalar da ke tattare da yin hakan.

Ya ce "daga gobe, 10 ga watan Yuni na shekarar 2020, za'a sassauta dokokin takaita zirga-zirga wanda hakan ke nuni da cewa Kaduna na kan hanyar komawa yadda take kafin wannan annobar."

Gwamnan ya ce a yanzu za'a iya fara yawo a cikin jihar, sai dai akwai dokar zama a gida daga karfe 8 na dare zuwa 5 na safe.

"Masu kasuwanci za su iya ci gaba da harkokinsu, sai dai dole sai an tabbatar da cewa akwai na'urorin gwajin zafin jikin dan adam, da kuma sinadarin kashe kwayoyin cuta da kuma bayar da tazara," in ji Gwamnan.

Sai dai ya ce har yanzu ba za a Iya bude kasuwanni da makarantu ba, amma za'a ci gaba da magana da masu ruwa da tsaki domin yanke hukuncin abinda ya kamata ayi.

A bangaren ibada kuma, ya ce masallatai da kuma coci-coci zasu iya kasancewa a bude a ranakun juma'a da kuma lahadi kawai.

Kana, gidajen gyaran gashi na maza da na mata ma za su iya budewa.

"Za a bayyana wa masu aikin gwamnati lokacin da za su koma bakin aiki."

A karshe gwamnan ya jadadda muhimmancin bin wadannan sharudan, ya kuma umarci 'yan jihar da su tabbatar da cewa sun gudanar da ayyukansu tare da kula da kansu, da kuma kaucewa yiwuwar yada cututtuka.

Jihar ta yi fama da dokar kulle ne domin takaita yaduwar cutar Coronavirus a cikinta.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG