Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Halin Rashin Tabbas A Kauyen Seytenga Na Burkina Faso Sakamakon Harin 'Yan Bindiga


‘Yan Bindiga
‘Yan Bindiga

Wasu hare hare da aka kai kwanan nan a kauyen Seytenga na kasar Burkina Faso sun yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da tilasta wa mutane kusan 3,000 tserewa daga matsugunansu, lamarin da ya sa masu nazari akan sha’anin tsaro suka fara jan hankalin gwamnatocin kasashen yankin.

SEYTENGA, BURKINO FASO - Rahotanni daga kasar Burkina Faso na cewa tun a ranar Larabar da ta gabata ne ‘yan ta’addan kungiyar HANI suka kai harin farko a garin Seytenga inda suka hallaka mutane 3 kafin su fice zuwa inda suka fito.

Wadannan mayaka sun kuma sake kai wani harin a washegari wato Alhamis inda a wannan karon suka afka barikin Jandarmomi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro 11 tare da lalata kayayaki da dama.

Rahotannin sun kara da cewa a ranar Juma’a wata bataliyar sojojin gwamnati ta isa garin na Seytenga, wace da farko zuwanta ya faranta ran al’umma da ke tsammanin dauki aka zo masu da shi kafin daga bisani murna ta koma ciki bayan da bataliyar ta umuruci ragowar sojojin garin su kwashe tarkacensu don kaura zuwa garin Dori, lamarin da ya firgitar da fararen hula suka gudu daga garin na Seytenga. Wasu bayanai sun ce garin ya fada hannun ‘yan ta’adda a ranar Asabar din da ta gabata.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi 12 ga watan Yuni, gwamnatin Burkina Faso ta tabbatar da cewa an yi fama da hare hare a makon da ya shude a garin na Seytenga sai dai ba ta yi bayani ba dangane da zahirin abubuwan da suka wakana da ma halin da ake ciki bayan kai wadannan hare hare, yayin da jaridun kasar ta Burkina Faso ke cewa sama da mutane 100 ne suka rasu daga ranar Laraba zuwa Asabar a garin na Seytenga.

La’akari da Kusancin yankin da aka fuskanci kashe kashen da iyakar Nijer ya sa masana jan hankali akan bukatar farfado da aiyukan hadin gwiwa a tsakanin wadannan kasashe 3 makwaftan juna, wato Nijer, Mali da Burkina Faso.

Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum, a yayin rangadin da ya kai a wasu kauyukan gundumar Tera da ke iyakar Nijer da Mali a karshen mako, ya shawarci shugabannin gwamnatin mulkin sojan Mali da Burkina Faso da su tsaurara matakan tsaro a iyakokinsu domin ta bangarensu ne ‘yan ta’adda ke samun sukunin watayawa yadda suka ga dama.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

An Shiga Halin Rashin Tabbas a Kauyen Seytenga Na Burkina Faso
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG