Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Rana Ta Biyu Da Tsai Da Wasu Harkokin Gwamnatin Amurka


Ganawar muhawara tsakanin Trump da Shugabannin Demokarat

A cigaba da kikikakar da ake yi tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump mai son gina katanga tsakanin Amurka da Mexico da kuma 'yan Demokarat masu adawa da bukatar ware kudin gina katangar a kasafin kudi, an shiga rana ta biyu da tsai da wasu harkokin gwamnati.

An shiga rana ta biyu a jere yau Lahadi, da wasu harkokin gwamnatin tarayyar Amurka su ka tsaya cik.

Wannan al'amarin ya shafi rubu'i, wato kashi 1/4 na bangaren gwamnatin tarayya mai kunshe da ma'aikatan gwamnati wajen sama da 800,000, wadanda fiye da rabinsu za su cigaba da aiki ba tare da ana biyansu ba.

Kafin Shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin tarayyar Amurka su sake kokarin cimma jituwa kan kasafin kudi, wanda ya haddasa wannan rigimar, sai bayan Kirsimeti, saboda gobe Litini da kuma jibi Laraba duk ranakun hutu ne na tarayya, bugu da kari, Majalisar Dattawan Amurka ba za ta zauna ba sai ranar Alhamis.

Kamar yadda aka sani, musabbabin wannan jan'in-jar shi ne batun samar da kudi don gina katanga a kan iyakar Amurka da Mexico. Shugaba Trump na son Majalisar Dokokin Tarayyar Amurka ta samar da dala biliyan $5.7 don gina katanga a kan iyakar Amurka da ke kudu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG