Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An shiga rana ta uku da fara taron yaki da cutar kanjamau na kasa da kasa


Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Rodham Clinton
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Rodham Clinton

Dubban wakilan kasashen duniya daban-daban na halartar babban taron kasa da kasa da aka soma a nan Washington akan yaki da cutar kanjamau

Dubban wakilan kasashen duniya daban-daban na halartar babban taron kasa da kasa da aka soma a nan Washington akan yaki da cutar kanjamau mai karya garkuwar jii ta AIDS/SIDA, wanda yau aka shiga rana ta ukku da soma shi.

A jawabin da tayi jiya awurin taron, Sakatariyar Ma'aikatar harkokin wajern Amurka Hillary Clinton tace Amurka ta daura damarar ganin cewa an sani al’ummar da bata da wannan cuta.

Saboda haka ne tace a shirye Amurka take ta tanadi mankudan kudaden da za’a yi anfani da su a kasashen Afrika da sauran kasashen wajen yakar wannan cutar, musamman don hana iyaye mata baiwa ‘yayansu jarirai wannan mummunar cutar.

Ta kuma yaba da wasu sababbin matakan yin kaciya da aka fito da su a kasashen Afrika dake hana wanzuwar daukar kwayar cutar ta HIV/AIDS a cikin hanzari.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG