Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Shiga Sabuwar Shekara A New Zealand, Australia


Wasan wuta mai tartsatsi a New Zealand
Wasan wuta mai tartsatsi a New Zealand

Yayin da agogon ya kai karfe 12 na dare a Australia, an saki abubuwan fashewa har tsawon minti 12 akan gadar Sydney Harbor da jama’a suka taru akai. don marabtar sabuwar shekara ta 2024.

Biranen Sydney da Auckland sun zama na farko cikin jerin mnyan biranen duniya da suk fara marabtar sabuwar shekarar 2024.

Sama da mutum miliyn daya ne suka yi dandazo don kallon wasan wuta mai tartsatsi a gabar kogin Sydney da kuma doguwar hasumiya nan ta Sky Tower da ke New Zealand

Yayin da agogon ya kai karfe 12 dare a Australia, an saki abubuwan fashewa har tsawon minti 12 akan gadar Sydney Harbor da jama’a suka taru akai.

A Auckland, babban birnin New Zealand, ruwan da aka yi ta yi a ranar jajiberi ya tsagaita tun gabanin a fara kidayar dakikokin da suka rage a shiga sabuwar shekarar.

Yakin da ake yi a Ukraine da Gaza da kuma zaman dardar da ake yi a sauran sassan duniya, na shafar bikin sabuwar shekarar ta hanyoyi da dama.

Birane da dama na kara tsaurara matakan tsaro, yayin da a wsu yankuna ma aka soke bikin na sabuwar shekara baki daya.

A birnin New York, jami’a da masu shirya taruka sun ce a shirye suke su tabbatar da tsaro ga dubban mutanen da za su taru a dandalin Times Square da ke tsakiyar yankin Manhattan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG