Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soma Harbe-harbe A Jamhuriyar Dimokradiyar Congo


Joseph Kabila wanda wa'adin mulkinsa ya kare jiya amma kuma ya ki shirya zabe ko sauka daga mulki
Joseph Kabila wanda wa'adin mulkinsa ya kare jiya amma kuma ya ki shirya zabe ko sauka daga mulki

Rahottani daga Junhuriyar Demokradiyar Congo sunce an wayi garin safiyar yau Talata da jin karar harbe-harbe suna tashi, kwana daya bayanda wa’adin saukar shugaban kasar Joseph Kabila daga karagar mulki, yazo, ya shige.

Da karfe goma-sha-biyun daren jiya Litnin din ne wa’adin mulki na biyu na shugaban ya kamalla, amma kuma wani kakakinsa, Barnabe Kikaya yace ce dole sai shugaban ya sauka daga mulki da karfe 12 na dare, kamata yayi a barshi ya wayi gari yana mulki.

Tuni dai Kotun Tsarin Mulki ta Congo ta yanke hukuncin cewa shugaba Kabila zai iya ci gaba da mulki har sai an yi sabon zabe, to amma sha-biyun dare na yi wasu mazauna birnin suka fara bushe-bushe don bada sanarwar cewa lokacin saukar shugaban fa ya zo.

An kama wani cikin wadanda suka fara zanga zangar kin amincewa da cigaba da shugabancin Joseph Kabila
An kama wani cikin wadanda suka fara zanga zangar kin amincewa da cigaba da shugabancin Joseph Kabila

Haka kuma an bada rahottanin jin karar harbe-harbe a yankuna da dama na kasar.

A cikin Kinshasha, babban birnin kasar, an yi tarukkan gangami da dama duk kuwa da haramcin irin wadanan tarukkan da gwamnati tayi.

An dai warwatsa sojoji ko ina cikin garin yanzu, yayinda ‘yan-sanda suka rinka watsa barknon tsohuwa don tarwatsa gungun mutanen dake zanga-zanga.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG