Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Soma Kidaya Kuri'un Zaben Ghana


Nana Akufo Addo dan hamayya da John Dramani Mahama shugaban kasa mai ci yanzu

Biyo bayan zantawar da Muryar Amurka tayi da mamban kwamitin cikin gida na kungiyoyin dake sa ido a lamuran zaben ya ce an soma samun sakamako daga sassa daban daban amma da wuya a ce ga wanda zai yi galaba sai an kammala kidayar duka.

Bisa ga yadda zabukan suka gudana musamman na shugaban kasa al'ummar Ghana sun fara yabawa shugabar hukumar zaben kasar wadda a can baya ake shakkar ko zata yi adalci.

Jama'a na ganin irin matakan da ta dauka da yadda ta shirya zabukan da yiwuwa a wannan karon kwalliya ta biya kudin sabulu. Ana ganin akwai inganci da adalci a zaben.

Yadda aka gudanar da zabe cikin lumana a Ghana
Yadda aka gudanar da zabe cikin lumana a Ghana

Wani abun da ya taimaka shi ne cikas da aka samu yayinda jami'an tsaro suka yi nasu zaben kafin ranar jiya. Hukumar zaben ta koyi daratsi a zaben kuma tayi gyaran da ya kamata tayi.

Yadda 'yan takaran biyu dake kan gaba suka je suka yi zabe da yadda tsohon shugaban kasar Jarry Rawlings ya yi nashi akwai tabbacin za'a samu sakamakon da 'yan kasar zasu amince dashi. Babu alamar magudi ko kadan.

Ga firar da Baba Yakubu Makeri yayi da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG