Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Ghana Mazauna Najeriya Na Fatan A Yi Zaben Kasarsu Lafiya


Gangamin zabe a Ghana

Yau 'yan kasar Ghana zasu yi zabi shugaban kasa tsakanin shugaba mai ci yanzu John Dramani Mahama da madugun 'yan adawa Nana Akufo Addo haka kuma zasu zabi 'yan majalisu

'Yan kasar ta Ghana dake zaune a Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu akan zabukan kasar tasu.

Wata Bariyatu Saidu daga Kumasi tayi fatan a fara zaben da sunan Allah a kuma gama da sunansa saboda shi Allah ya riga yayi nashi zabin. Amma idan so samu ne suna fatan Allah ya maida shugaba mai ci yanzu kan mukamin.

Shi ma Ibrahim Tanimu yana fatan a yi zaben lafiya a kare lafiya ba tare da tashin hankali ba.

Yakubu Sha'aibu yace suna fatan alheri game da zaben. Idan an yi zaben lami lafiya to an yiwa al'ummar Afirka ne saboda irin rikice rikicen da ake fama dasu a kasashen duniya daban daban..Ya kira 'yan kasar su kai zuciya nesa su yi zabe cikin lumana kuma duk wanda Allah ya ba a amince dashi.

Shabari Ibrahim shi ma yace suna fatan su ga zaben ya gudana cikin lumana da adalci da fatan Allah ya zaba masu shugaba nagari.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG