Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tilasta Wa Mazauna Gabar Kogin Binuwai Barin Gidajen Su


.

Biyo bayan gargadin da hukumomin kasar Kamaru suka yi na cewa zasu sako ruwa daga madatsar ruwan Lagdo dake yankin arewacin kasar yanzu haka,rundunan yan sanda a jihar Adamawa dake makwabtaka da Kamaru sun gargadi al’ummomin dake zaune a gabar kogin Binuwai da su hanzarta tashi kafin nan da ranar jumma’a.

A sanarwar da rundunan yan sandan jihar Adamawa daya daga cikin jihohin da ambaliyar ka iya shafa ta fitar,rundnar ta gargadi al’ummomin dake zaune a gabar kogin Binuwai da su hanzarta tashi don gudun ambaliyar da ka iya aukuwa.Ko a shekarar 2012,rayuka da dama ne suka salwanta baya ga dukiya na miliyoyin naira,biyo bayan sako ruwan da hukumomin kasar Kamarun suka yi.

DSP Habibu Musa Muhammad mukaddashin kakakin rundunar yan sandan jihar Adamawa,ya ce ana bukatar wadanda ke zaune a gabar kogin da ya shafi jihohin Adamawa,Taraba,Binuwai da kuma jihar Kogi da su hanzarta tashi.

Yan majalisar kasar dai na ganin dole mahukuntan Najeriya suma su dau mataki ta hanyar gina manyan madatsur ruwa. Hon. Yusuf Captain Buba,wani dan majalisar wakilai a Najeriya ya bada shawarar cewa bude madatsar ruwa shi zai taimaka.

Saurari rahoton IbrahimAbdulaziz domin karin bayani...

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG