Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tilastawa Masu Gadin Gidan Yarin Da Epstein Ya Mutu Zuwa Hutu

Dan shekaru 66 da haihuwa Epstein yana fuskantar shari’a kan tuhume tuhuman gwamnatin tarayya na safarar mata da ake lalata da su da ya hada da yara mata kanana da wasunsu shekarun su bai gaza goma 14.

Atoni Janar din Amurka, William Barr, ya ba da umurnin a sa wasu masu gadin su biyu, da su tafi hutu daga gidan yarin tarayya nan da attajirin nan Jeffrey Epstein ya kashe kansa.

Dan shekaru 66 da haihuwa Epstein yana fuskantar shari’a kan tuhume tuhuman gwamnatin tarayya na safarar mata da ake lalata da su da ya hada da yara mata kanana da wasunsu shekarun su bai gaza goma 14.

Sai dai an tsinci Epstein ya kashe kansa a ranar Asabar yayin da yake tsare.

Ana zargin ya rataye kansa ne da zanin shimfidar gado a cikin dakin da yake tsare inda yake jira a yi masa shari’a kan zargin cin zarafin yara ‘yan mata kanana.

An dai cire Epstein a cikin jerin wadanda ake saka wa ido saboda kada su kashe kansu a gidan yarin da yake birnin New York a watan da ya gabata, ba tare da bayyana wani dalili kwakkwara ba, amma akwai umurnin da aka bayar ga masu gadi da su rika duba shi bayan kowanne minti 30.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG