Masu zanga zangar adawa da gwamnati a kasar Algeria, sun yi biris da alkawarin da shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika ya yi, na cewa zai yi dan takaitaccen wa’adi ne, idan aka sake zaben shi a watan Afrilu.
A jiya Litinin, an yi ta zanga, wacce matasa suka jagoranta, tare da kauracewa ajujuwansu na jami’o’i a Algiers, babban birnin kasar.
Sabuwar zanga zangar ta barke ne sa’a guda bayan da ofishin shugaban kasar ya mika takardunsa na neman yin takarar neman wa’adi na biyar a zaben da za a yi a watan gobe.
A Faransa ma, ‘yan kasar ta Algeriya, sun gudanar da zanga zanga, inda akalla mutum dubu shida suka yi gangami a wani dandali da ke birnin Paris a ranar Lahadi, inda suka yi ta furta kalaman batanci akan shugaba Bouteflika mai shekaru 82, wanda ke fama da rashin lafiya, tun bayan da ya samu matsalar shanyewar barin jikinsa a shekarar 2013.
Facebook Forum