Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tsare Wani Alhajin Nigeria Domin Ya Dauki Abin Tsintuwa A Harami.


HAJJ 2016
HAJJ 2016

Hukumomin tsaro sun tsare wani Alhaji Dan Nigeria sakamakon daukar wani abinda ya tsinta a harabar Harami

Jami’an tsaron Haramin Makka sun cafke wani Alhajin Nigeria da ya sunkuya ya dauki wani abin tsintuwa a harabar Haramin.

Da yake bayyanawa wakilin Muryar Amurka yadda abin ya faru, karamin jakadar Najeriya a Saudi Arabia, Alhaji Sani Yunusa yace akwai kyamarori fiye da dubu biyu a Masallacin da kewayen sa, wadanda ke nuna dukkan abinda ke faruwa a ciki da harabar masallacin.

Don haka Alhaji Yunusa ya shawarci Alhazzai da su gujewa daukar duk wani abu da suka ga ya fadi a Haramin domin tsira da martabar su, kuma da gudun mummunar fahintar tsintuwar.

Haka kuma karamin jakadar ya zagaya gidajen Alhazan Najeriya domin yi musu wannan gargadin, yana cewa ta haka ne Alhazan na Nigeria zasu tsira da kimar su da martaban su.

Ga Nasir Adamu El-Hikaya da Karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG