Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tuhumi Tsohon Shugaban Brazil Da Laifin Sarrafa Kudaden Haram


An tuhumi tsohon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva da laifin sarrafa kuddade ta hanyar haram da kuma cin hanci da rashawa.

Jami’an binciken tarayya ne suka bada sanarwar wannan tuhumar da ake wa tsohon shugaban a jiya Laraba, wacce suka ce tana da nasaba da wani binciken da aka gudanar a Kampanin man fetir ta kasar mai suna Petrobras.

An zargi tsohon shugaban da matarsa da wasu mutane da dama da cin moriyar kudin kashe mu raba na gyaran wasu gidaje nab akin teku da wani kampanin gine-gine mai alaka da Petrobras suka gina. Lula ya musunta wannan zargin yana cewa ba shi keda wannan kadarar ba.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG