Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Wayarwa Da Jama'a Kai Kan Muhimancin Aikin Tafkin Mambila


An gudanar da taron wayar da kan jama'a akan muhimancin madatsar ruwa ta Mambila.

Taron an shirya shi ne da zimmar fadakar da al'ummar yankin game da hatsuran da ke akwai a wannan aiki na madatsar ruwan Mambilla.

A bayyanawa jama'a fa'idar da ke akwai kana kuma da manyan kayayyakin aiki da za'a zo da su da hakan ya sa aka gargadi jama'a da su kula.

Gwamnan jihar Taraba Akitet Darius Isiyaku wanda Kwamishinan makamashi Hon. Garba Wanda ya wakilce shi ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da hadin kai don ganin an samu nasarar aiwatar da aikin.

"Babban abin da ya kawo mu shi ne mu wayarma jama'a da kai, akan muhimancin wannan tabkin, haka kuma kada jama'a su yi dogaro da irin labaran da ake ba su na tsoratarwa dangane da tabkin, kokarin gwamnati shi ne ta ga cewar al'uma sun ci gajiyar tabkin." a cewar wakilin gwamna Darius.

Shi ma a jawabinsa Ministan makamashi Engr Sale Mamman, wanda hadiminsa Hon. Emmanuel Bello ya wakilce shi a wannan taro da ya hado sarakuna, da sauran masu ruwa da tsaki ya zayyano manufar wannan shiri da cewa.

Ya kara da cewa za su tabbatar an biya jama'ar yankin hakokinsu na diyya akan filayensu da aka karba, yana mai cewa hakin da yanzu ya rataya akan Sarakuna shi ne su wayar da kan jama'a hanyoyin da za su bi don karbar hakokinsu.

Wannan madatsar ta Mambila za ta taimaka matuka wajen kara inganta tattalin arzikin yankin idan aka kammala shi a cewar mahalarta taron.

Ga rahoton Ibarhim Abdul'aziz a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG