Accessibility links

An kamo wani mutum da ake Zargi da yan-yanka wata yarinka gunduwa-gunduwa domin yin kudi.

Rundunar 'yan sandan jihar Oyo ta samu nasarar kame wani da ya kashe wata yarinya 'yar shekaru shida wanda yayi gunduwa-gunduwa da ita don ayi masa kudi.

Mataimakin kwamishina 'yan sandan jihar mai kula da sashen 'yan sanda ciki a jihar ta Oyo, Dasuki Galadanchi ne yace an kama mai laifin a birnin Sokoto a wata hira da yayi da wakilin Muryar Amurka Hassan Umaru Tambuwal.

Mr. Galadanchi yace ”ana cikin binciken neman yarinya sai aka ji wari daga wani gida, da aka je aka bincika sai aka gano cewa ita yarinyar da ake nema ne aka yi gunduwa-gunduwa da ita, aka sakata a cikin wata roba.”

"Masu dakin kuwa aka neme su aka rasa, amma hoton sa da aka samu a dakin shi yasa aka gano wanda ya aikata wanna mugun aikin", a cewar Mr. Dasuki Galadanchi.

Wanda ake zargi da aikata wanna aika-aika mai suna Yusuf Biodun Nasiru, cewa yayi "wani dattijo ne ya bukacesu dashi da dan dattijon da su kashe yarinya domin ayi maganin kudi da ita.”

Mataimakin kwamishinan 'yan sandan yayi kira ga iyayen yara dasu tabbatar da cewa an kaisu da kuma dawo dasu daga makarata masamman yara kanana.

XS
SM
MD
LG