Accessibility links

Mahaifin yarinyar ya furta da bakinsa cewa lallai yana kwanciya da ita, da ma yayarta, yana mai cewa wani boka ne ya sanya shi yin hakan domin ya zamo mai kudi

'Yan sanda a Jihar Gombe su na ci gaba da binciken lamarin wani mutumi mai suna Abubakar Tahir, wanda diyarsa ta kai karar cewa yana lalata da ita karfi da yaji, bayan da aka ce sauran 'yan'uwanta da ta kai maganar wurinsu sun kasa kawo karshen wannan lamarin.

Kakakin 'yan sandan Jihar Gombe, DSP Attajiri, yace lallai su na rike da wannan mutumin wanda ya amsa zargin cewa lallai yana kwanciya da diyar tasa mai shekaru 14 da watanni.

Bayan nan ma, mutumin ya furta da bakinsa cewa yayi lalata da diyarsa ta farko ma, yayar wannan ta yanzu, kafin ta yi aure, duk a bisa cewar wai boka ne yace masa yayi hakan domin ya zamo mai arziki.

Yace da zarar sun gama bincikensu, zasu gabatar da wannan mutumi a gaban kotu.

Da yake magana da 'yan jarida a lokacin da aka gabatar da shi, wannan mutumi mai lalata da 'ya'yan nasa, Abubakar Tahir, yace ba zai iya tuna ko sau nawa ya kwanta da 'ya'yansa mata ba, amma yace yayi hakan ne bisa zaton zai yi arziki kamar yadda yace wani boka ya fada masa.

Shi wannan boka mai suna Mohammed Ibrahim, ya karyata cewa ya fadawa Abubakar Tahir ya rika kwanciya da 'ya'yansa, yana mai cewa shi dai ya tambaye shi maganin karfin maza ne kawai, kuma ya ba shi.

Wasu lauyoyin kare hakkin bil Adama masu zaman kansu, sun shiga cikin wanan lamarin domin tabbatar da cewa an hukumta wannan mutumin a saboda danyen aikin da ya aikata.
XS
SM
MD
LG