Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yanke Ma Tsohuwar Shugabar Koriya Ta Kudu Daurin Shekaru 24


Tsohuwar Shugaba Park Guen-hye
Tsohuwar Shugaba Park Guen-hye

A karshe dai an yanke ma tsohuwar Shugabar Koriya Ta Kudu daurin shekaru 24 a gidan yari saboda samunta da laifin cuwa-cuwa da kuma amfani da ikon mukaminta ba bisa ka'ida ba.

Wata kotun Koriya Ta Kudu ta zartas da hukuncin daurin shekaru 24 ma tsohuwar Shugabar Koriya Ta Kudu Park Geun-hye, bayan da kotun ta same ta da laifin amfani da ikonta ba bisa ka’aida ba da kuma almundahana.

Yayin yanke hukuncin, wanda aka yada ta gidan talabijin na kasa, Kotun Gundumar Tsakiyar Seoul ta sami Park da laifin karbar cin hanci da kwace da amfani da iko ba bisa ka’ida ba da kuma wasu tuhumce-tuhumcen dai. Babban Alkalin Kotun y ace ya zama wajibi a yi tuhumar gaske ma tsohuwar Shugabar “saboda laifin da ta tafka, ko ma don ya zama darasi ga duk wani Shugaban da zai yi amfani da ikon da jama’a su ka bashi ba bisa ka’ida ba, da kuma haddasa rudami a harkokin da su ka shafi kasa.”

Baya ga hukuncin daurin, an kuma ci Park tarar fiye da dala miliyan 16. Tsohuwar Shugabar ta Koriya Ta Kudu na iya daukaka kara cikin mako guda. Park dai ta tsaya kai da fata cewa ita fa ba ta aikata wani laifi ba, ta na jaddada cewa ramuwar gayyar siyasa ce kawai ta rutsa da ita. Masu gabatar da kara sun so a zartas ma ta da hukuncin daurin shekaru 30.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG