Wani alkalin kotun gwamnatin tarayya na Amurka ya yankewa tsohon shugaban yakin neman zaben shugaba Donald Trump hukuncin daurin watanni 47 a kurkuku akan laifukan da suka shafi haraji da ajiya a banki.
Hukuncin bai kai tsawon shekaru 19 zuwa 21 da lauyoyi masu gabatar da kara suka so a yanke mashi ba, abinda kusan ke nufin da Manafort, mai shekaru 69 zai kasance a gidan yari har karshen rayuwar sa.
Alkali T.S. Ellis ya ce ka’idodin yanke hukunci na gwamnatin tarayya, da kuma hukunci mai tsanani da mai bincike na musamman Robert Mueller ya nemi a ba Manafort yayi zafi sosai.
Alkali Ellis ya kuma bayyana cewa ba Manafort ba ne makasudin binciken da Mueller ke yi ba, wato binciken ko kwamitin yakin neman zaben Trump ya tuntubi Rasha akan zaben shekarar 2016.
Za ku iya son wannan ma
-
Afrilu 09, 2021
Mawakin Gambara DMX Ya Mutu
-
Afrilu 09, 2021
Dan Najeriya Da Ya Zama Kyaftin Din Jirgin Yakin Ruwan Amurka
-
Afrilu 03, 2021
An Kashe Wani Dan Sandan Ginin Majalisar Dokokin Amurka
-
Maris 31, 2021
Kakar Barack Obama Ta Rasu
Facebook Forum