Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Masu Rajin Kare Damokaradiyya Na Kasar Hong Kong Hukuncin Dauri


The White House
The White House

"Amurka ta yi Allah wadai da hukuncin da aka yanke wa shugabanni bakwai masu rajin kare dimokiradiyya da ke da nasaba da siyasa," a cewar Sakatariyar Harkokin Wajen Antony Blinken. An tuhume su ne da laifin shiga cikin zanga-zangar lumana a shekarar 2019 na nuna kin amincewa da cin amanar da China ke yi wa 'yancin Hong Kong.

Shugabannin masu rajin kare dimokiradiyya da aka yanke wa hukuncin sun hada da Martin Lee, Jimmy Lai, Albert Ho, Margaret Ng, Cyd Ho, Lee Cheuk-yan, da Leung Kwok-hung. Biyar daga cikin wadanda ake tuhumar sun sami hukuncin zaman kurkuku na watanni takwas zuwa 18, wasu kuma an yanke musu hukuncin da aka dakatar, ciki har da shugaban da ya kafa jam'iyyar Hong Kong Democratic Party, Martin Lee. Sakatare Blinken ya kira hukunce-hukuncen "wadanda ba su dace da yanayin tashe-tashen hankali ba na ayyukan shugabannin masu rajin kare dimokiradiyya."

Wasu daga cikin masu fafutuka, kamar su Jimmy Lai, dan shekaru 73 da ya kafa wata jarida mai rajin kare dimokiradiyya a Hongkong, na fuskantar karin tuhume-tuhume, ciki har da karkashin wata babbar dokar tsaron kasa da China ta sanya wa Hong Kong a shekarar 2020, wacce ta ba da damar fadada ikon China don fatattakar ire-iren laifukan siyasa da ake zargi.

Sakatare Blinken ya yi tir da hukuncin da aka yanke wa masu rajin kare dimokiradiyya da cewa “wani misali ne na yadda [Jamhuriyar Jama'ar China da mahukuntan Hong Kong ke tauye hakkokin da 'yanci da Dokar Asali na Sanarwar hadin gwiwa tsakanin China da Burtaniya ta tabbatar don kawar da duk wani nau'i na rashin yarda. ”

Sanarwar Hadin gwiwar China da Birtaniyya, wata yarjejeniya ce ta kasa da kasa, wanda ta ba da tabbaci ga Hong Kong wani babban ikon cin gashin kai, kuma ya kamata alumm'ar Hong Kong su sami 'hakki da' yanci da aka ba da tabbaci a cikin Sanarwar hadin gwiwa da Dokar Asali.

Amurka za ta ci gaba da mara wa ‘Yan Hong Kong baya yayin da suke mayar da martani kan harin da China ta kai musu kan‘ yanci da cin gashin kansu kuma za ta ci gaba da kira da a saki wadanda ake tsare da su ko kuma suke tsare a kurkuku saboda gudanar da muhimman ‘yancinsu.

XS
SM
MD
LG