A yau Laraba, wani alkali a kotun Mumbai ya yanke hukuncin bayan da aka same sa da laifin.
A baya Khan ya fuskanci tuhumar zaman gidan yari na tsawon shekaru goma ne.
Masu gabatar da kara sun yi zargin cewa Khan ya sha barasa ne a lokacin da motarsa kirar Toyota ta abka kan wasu mutane biyar da ke bacci a gefen titi, inda nan take guda ya mutu sannan hudun suka samu raunuka.
Khan mai shekaru 49, ya musanta cewa shi ke tuka motar a lokacin da hadarin ya faru, ana kuma sa ran zai daukaka karar a kotun da ta ba damar yin hakan.
Fiye da sheakru 12 ke nan aka kwashe ana wannan shari'a sai a wannan karo aka yanke mai hukunci.