Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yankewa Wasu Hukuncin Kisa a Iraqi


[FILE]
[FILE]

Wata kotu a Iraqi, ta yanke hukuncin kisa akan wasu mayakan tsageru su 24, bayan da aka same su da hanu a kisan da akawa sojojin kasar a Tikrik a shekarar da ta gabata.

Daruruwan mayakan sa kai da sojin kasar ta dauka, wadanda mafi yawansu mabiya mazhabar Shi’a aka kashe, bayan da kungiyar IS ta karbe wani lardi da ke dauke da wani sansanin soji.

Kotun dai ta bayyana cewa za a aiwatar da hukuncin kisan ta hanyar rataya, yayin da ta wanke wasu mutane hudu daga zargin, bayan da aka kasa kafa hujja a kansu.

A wancan lokacin bazarana ne, mayakan IS suka karbe ikon birnin na Tikrit, wanda ya kasance mahaifa ga tsohon shugaban kasar Saddam Hussein da aka kashe.

Amma tun a lokacin dakarun Iraqi suka fatattaki mayakan daga birnin, tare da samun taimakon mayakan ‘yan Shi’a.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG