Accessibility links

An Yankewa 'Yan Muslim Brotherhood Hukuncin Kisa


Mata 'yan uwan wadanda aka yankewa hukuncin kisa, a kasar Masar. Afrilu 28, 2014

​Wata Kotu a kasar Misra, ta yanke hukuncin kisa a kan ‘yan kungiyar ‘yanuwa Musulmi da ake kira Muslim Brothers su wajen 683 saboda samunsu da laifin aikata kisan wani babban jami’in dan sanda.

Yau litinin alkalin kotun ya yanke hukuncin a wani zama na musamman da kotun tayi a Minya dake da tazarar kilomita metan (200) Kudu da birnin Alkahira.

An jingina laifin da tarzomar da ta biyo bayan zanga-zangar da aka yi a Minya wadda ta juye ta koma tashe-tashen hankula bayan da aka yi fito na fito tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaron Misra a watan Agustan da ya gabata.
XS
SM
MD
LG