Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Ambaliyar Tabo A Tsibirin Java Dake Indonesia


A tsibirin Java dake kasar Indonesia jami’an Agajin gaggawa sun ce kusan mutane 12 ne kasa ta binne a yau Asabar wasu kuma ba’a gansu ba, a wanizamiyar kasar da ruwan sama ya jawo

Amma har izuwa yanzu ba’a san adadin mutanen da abin ya shafa ba.Jami’an sun ce Ambaliyar tabon ta afku a kauyuka ne inda mutane ke girbin Citta inda ya binne gidaje kusan 30.

Masu agajin gaggawa da jami’an ‘Yan sanda na neman mutanen da suka bata.

Jami’ai sun kara da cewar wasu daga cikin mazauna kauyukan sun dawo gida a yau Asabar din bayan kwashe dare da sukayi a matsugunnai na gaggagawa saboda gargadin yiwuwar ambaliyar da ruwan sama mai tsananin yawa a kwanakin nan ya haifar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG