Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Amfani Da Harbin Bindiga Wajen Tarwatsa Masu Zanga-zanga a Congo


Jiya Juma’a ‘yan sanda a kasar Dimokaradiyar Congo sunyi harbin gargadi saboda su tarwatsa wasu matafiya coci da suka taru domin makokin mutane bakwai da aka kashe lokacin zanga-zangar kin jinin shugaban kasa Joseph Kabila.

Wakilin Muryar Amurka na sashen Faransancin Afirka, ya ce ‘yan sandan suna ‘dauki matakin ne bayan da ‘dinbin mutanen dake barin wata Majami’a suka fara fadin wasu kalaman batanci ga shguaba Kabila. ‘Yan sandan sun harba barkonon tsowuwa, suka kuma kara da harbin gargadi.

Mutane biyu sun raunata, yayin da dinbin jama’a suka ruga ta ko ina.

A lokaicin da suke cikin Majami’a, shugabannin Majami’ar Catolika sun yi kira ga Kabila da ya mutunta yarjejeniyar da Majami’a ta taimaka aka cimma a siyasance, wadda ta yi kira ga shguaban kasa ya gudanar da zabe ya kuma sauka daga kan mulki.

Sama da shekara guda kenan Kabila ya ci gaba da zama kan mulki bayan cikar wa’adinsa na biyu, wanda ke zama wa’adi na karshe da kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Dimokadiyyar Congo ya bashi. Jami’an tsaro sun budewa masu zanga-zangar kin jinin Kabila wuta a babban birnin kasar ana jajiberan sabuwar shekara, inda suka kashe mutane bakwai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG