Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi arangama da yan sanda yayinda dubban mutane suka yi zanga zanga a birnin London


Masu zanga zanga a birnin London

An yi arangama da yan sanda yayinda dubban mutane suka yi zanga zanga a birnin London

Masu zanga zanga da suka rufe fuskokinsu sun yi arangama da ‘yan sandan kwantar da tarzoma, suka kai hari kan bankuna da shaguna da kuma otel otel a birnin London jiya asabar, suka dishe kaifin zanga zangar lumanar da sama da mutane dubu dari biyu da hamsin suka gudanar na nuna adawa da matakin da gwamnatin Birtaniya ta dauka, na rage kudaden da take kashewa wajen samar da ababan jin dadin rayuwa. Yan sanda sun ce sun kama sama da mutane maitan, da dama kuma suka ji raunuka yayinda masu zanga zangar suka rika wurga kwalabe, suna kuma jifar ‘yan sandan da harsashen wuta da kuma wadansu ababa. Wannan gumurzun ya dauke hankalin jama’a daga zanga zangar lumana da aka fara ta adawa da tsuke bakin aljihun gwamnati, da Karin kudin haraji da kuma yiwa tsarin fansho garambawul. Birtaniya tana shirin rage dala miliyan dubu dari da talakin daga kudaden da take kashewa, yayinda gwamnati ke kokarin rage gibin kasafin kudin da kasar ke fama da shi. Kungiyar kodago ce ta shirya zanga zangar, wadda tace zaftare kudin da gwamnati ke kashewa zai maida hanun agogo baya, a yunkurin farfado da tattalin arziki, ya kuma bata sunan kasar Birtaniya. Wannan ce zanga zanga mafi girma da aka gudanar a babban birnin kasar tun bayan zanga zangar da aka gudanar cikin shekara ta dubu biyu da uku ta nuna adawa da yakin Iraq.

XS
SM
MD
LG