Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Asarar Sama Da Naira Tiriliyan Guda A Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya


Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya

An yi asarar dinbin kudi a kasuwar hannayen jarin Najeriya, al'amarin da wasu kwararru ke dangantawa da matakan gyara kasa da gwamnati mai ci ke daukawa

Ga dukkan alamu sai Hukumar Kasuwar Hannayen Jarin Najeriya ta biya diyyar kudi mai yawan gaske ga masu saka jari saboda faduwar da hannayen jarinsu su ka yi sanadiyyar dalilan da akan alakanta su da matakan da gwamnatin Najeriya ta dauka musamman don ceto Naira, wacce darajarta ke ta faduwa.

Wadanda aka tantance asarar da su ka yi, wadanda sun kai kusan dari hudu, sun yi asarar wajen sama da Naira biliyan dubu bisa ga alkaluman da su ka bayyana a watan jiya. Haka zalika wasu kwararru na alakanta faduwar darajar hannayen jarin daga sama da Naira tiriliyan goma sha daya zuwa tiriliyan goma da jinkiri wajen nada Ministoci. Wani jami’I a hukumar sai da hannayen jari mai suna Ahmadu Manu ya ce duk wadanda su ka zuba jarinsu don su yi riba, da zarar an samu matsalar tsaro su kan kwashe dukiyarsu don kar su yi asara.

Shi kuwa wani masanin tattalin arziki mai suna Hashimu Muhammed ya danganta faduwar darajar hannayen jari da matsalar wutar lantarki gami da rashin tabbas kan makomar kasar. To amma y ace Najeriya ta kama hanyar magance matsalar game da sauran matsaloli saboda shi kansa Shugaban kasar ba mai cin hanci na be.

Labarin Nasiru Adamu Elhikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG