Accessibility links

An Yi Bukin Ranar Ma’aikata Ta Duniya A Ghana Cikin Yanayin Yajin Aiki

  • Grace Alheri Abdu

Shugaban Kasar Ghana's President John Dramani Mahama
Ma’aikata a kasar Ghana sun shiga sahun takwarorinsu na kasashen duniya wajen gudanar da bukukuwan ranar ma’aikata ta duniya.

An gudanar da bukukuwan ne a yanayin yajin aiki inda kungiyoyin ma’aikata da dama suke yajin aiki da suka hada da ma’aikatan kiwon lafiya da suke yajin aiki a halin yanzu sabili da wadansu dalilai da suka jibinci albashinsu.

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama yana daya daga cikin manyan bakin da suka halarci bukin na bana mai taken “kudin fansho hakinka ne amma nauyi ne a wuyanka”
Wakilinmu Baba Yakubu Makeri ya bayyana cewa, taron ya sami kyakkyawar halarta duk da ruwan sama da aka rika tafkawa.
XS
SM
MD
LG