Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Dokar Rabawa Amurkawa, Kamfanoni Tiriliyan 2


Shugaba Donald Trump yarin da yeke rattaba hannu kan dokar
Shugaba Donald Trump yarin da yeke rattaba hannu kan dokar

Sa’o’i bayan da Majalisar Wakilan Amurka ta amince da kudurin fitar da sama da dala Tiriliyan 2 domin tallafawa tattalin arzikin Amurka da ke fuskantar barazanar tabarbarewa sanadiyyar cutar COVID-19, Shugaba Donald Trump ya rattaba hannu kan kudurin - wanda yanzu ya zama doka.

Wadannan kudade, sune mafiya yawa da gwamnatin Amurka ta taba fitarwa a matsayin tallafi a tarihin kasar, matakin da ya nuna tsananin yanayin da annobar ta coronavirus ta haifar.

“Ina so na mika godiya ta ga ‘yan Democrat da ‘yan Republican da suka hada kai domin nuna kishin kasa.” Trump ya ce a bikin rattaba hannu kan kudurin a ranar Juma'a.

“Ban taba rattaba hannun kan kudin da yawansu ya kai tiriliyan ba.” Shugaban na Amurka ya kara da cewa.

A cewar shugaban masu rinyaje a majalisar dattawa, Mitch McConnell, “wannan lokaci ne da za mu yi alfahari,” yana mai jinjijina yadda jam’iyyun biyu suka hada kai aka amince da kudurin.

Daga cikin abin da za a yi da kudaden, za a rabawa Amurkawa da asibitocin da suka galabaita sanadiyyar cunkoson masu cutar da kuma kamfanonin inshorar lafiya.

Baya ga haka, za a baiwa kananan masana’antu da manyan kamfanoni basuka domin su rage radadin dakatar da ayyukansu da ma'aikatansu da suka yi sanadiyyar cutar ta COVID-19.

Kamfanoni, ma'aikatu da shagunan kasuwanci da dama a Amurka, sun dakatar da ayyukansu bayan da masana kiwon lafiya da hukumomi suka ba da shawarar yin hakan domin a dakile yaduwar cutar ta coronavirus.

Rahotanni baya-bayan nan sun tuna cewa Amurka ce ta fi kowacce kasa yawan wadanda suka harbu da cutar.

Adadin wadanda Suka kamu da ita ya haura mutum 100,000 sannan kusan mutum 1,500 sun mutu - 366 daga cikinsu a birnin New York.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG