Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Fyade Sama da 120 a Katsina Cikin Watanni 3


Wata budurwa da aka yi wa fade

A Najeriya fade ma yara kanana na neman zama tamkar wani abin alfahari. Da wuya a yi mako guda ba tare da jin wani labarin aikata fade ba a nan da can; kuma ‘yan rajin kare wadanda aka yi wa fade sun ce idan aka yi kara guda game da fade, to labudda akwai kuma wasu ayyukan fade sama da takwas da iyaye su ka boye.

A hira da gidan rediyon Muryar Amurka, kakakin rundunar ‘yan sandan jahar Katsina, Sufurtandan Gambo Isa ya ce daga watan Afiliru zuwa watan Yunin da ya gabata an kama wadanda su ka yi wa yara kanana fade da luwadi mutum sama da arba’in. Daga watan daya kuma na Janairu zuwa watan Yuni din an kama mutun 120 da su ka aikata wannan laifin.

Da aka tambaye shi game da zargin da ake cewa ‘yan sanda kan ja kafa wajen binciken wadanda ake zargi da laifin aikata fade, sai ya ce ba haka abin yake ba. Ya ce laifin fade na da girma; hasali ma, yana cikin rukunin manyan laifuka irinsu fashi da makami da kisan kai. Bugu da kari, doka ba ta bai wa DPO damar zama a ofishinsa ya saurari irin wannan karar ba. Kwamishinan ‘yan sanda ne kadai ke da hurumin bibiyar batun daga ofishinsa.

FILE - A woman carries a placard as she shouts a slogan during a "Walk Against Rape" march in Lagos, Nigeria, Oct. 5, 2011.
FILE - A woman carries a placard as she shouts a slogan during a "Walk Against Rape" march in Lagos, Nigeria, Oct. 5, 2011.

Zanga zangar yin tir da fade.

Sufurtanda Gambo ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jahar Katsina, alal misali, ya sha gaya wa masu ruwa da tsaki a zama da yak e yi da su na wata wata cewa duk wani zargin aikata fade ba zargi ne da ake yafewa ba; ba kuma zargi ne da za a iya zama da DPO da Mai Unguwa a sasanta a kai ba. Irin wannan zargin dole ne a gabatar da shi gaban Kwamishinan ‘yan sanda kuma daga bisani a kai kotu. Kuma idan an kai batun kotu, Kwamishinan ‘yan sandan kan bi diddigin shari’ar ta wajen sawa a kawo masa takardun bayanan yadda ake gudanar da shari’ar da kuma inda aka kwana.

Ya ce duk da cewa a yanzu gidajen yari sun daina karbar mari irin wannan laifin saboda matsalar cutar corona, an ware masu wuri musamman ma a hedikwatar ‘yan sandan jahar Katsina mutum sama da hamsin.

Bincike ya nuna cewa akasarin lokuta ana yi wa yara kanana fade ne saboda dalilai na tsafi – musamman don neman dokiya ko mukami. Akwai kuma masu budurwar zuciya. Su ma iyaye, musamman ma masu tura ‘ya’yansu talla ba tare da lura da take takensu da kuma lokacin da su kan dawo gida ba, su na da irin nasu laifin.

Ga Sani Shu’aibu Malumfashi da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:48 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG