Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Girgizar Kasa Mai Karfi A Gabashin Japan


Girgizar Kasa A Japan
Girgizar Kasa A Japan

Wata girgizar kasa mai karfi ta afku a gabashin kasar Japan a yammacin ranar Juma’a, kamar yadda kafar yada labarai ta NHK ta bayyana.

Girgizar kasar mai karfin maki 6.2 ta faru ne da misalin karfe 10:03 na safe agogon GMT, a cewar hukumar nazarin yanayi ta kasar Japan. Girgizar ta jijjga gine-gine a birnin Tokyo da kuma wasu larduna da ke kewaye, amma ba a samu rahoton barna ba nan take.

Girgizar ta fara ne a kusa da lardin Chiba, a gabashin Tokyo, a zurfin kilomita 50. Hotuna daga kafar labarai ta NHK sun nuna gine-gine na girgiza a kusa da filin jirgin saman Narita na Chiba. Hukumomin filin jirgin saman na nazari su ga ko girgizar ta lalata titin jiragen sama na tashar, in ji NHK.

Girgizar kasar Japan
Girgizar kasar Japan

Kamfanin Jirgin Kasa na East Japan ya ce ya dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a lardin Chiba.

Girgizar kasa ta zama ruwan dare a kasar Japan, daya daga cikin yankunan da suka fi yawan samun girgizar kasa a duniya. Kasar Japan ce ke da kusan kashi daya bisa biyar na girgizar kasa mai karfin maki 6 ko kuma sama da haka.

A ranar 11 ga watan Maris na shekarar 2011, girgizar kasa mai karfin maki 9 ta afku a gabar tekun arewa maso gabashin kasar, wadda ita ce girgiza mafi karfi da aka taba yi a Japan, da kuma bala'in tsunami mai girma.

bala'in Tsunami
bala'in Tsunami

Kafar NHK ta ce kamfanin wutar lantarki na Tokyo na nazarin ganin ko akwai alamun wani abu ya lalace a cibiyar makamashin nukiliya da ke Fukushima, wurin da aka samu barna sosai a girgizar kasar da ta auku a shekarar 2011.

XS
SM
MD
LG