Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Girgizar Kasa Mai Karfin Maki 7.2 A Mexico


Mutane suna kallo bayan girgizar kasa a Mexico ,

An yi wata gagarumar girgizar kasa a kasar Mexico jiya jumma’a da tayi barna a jihar Oaxacaq, sai dai babu rahoton jin raunuka ko kuma rasa rayuka.

Girgizar kasar mai karfin maki bakwai da digo biyu ta faru ne a wani kauyen jihar dake kudanci kusa da gabar taken pacific da kuma iyaka da jihar Guerrero.

Jami’ai sunce girgizar kasar tayiwa wadansu gidaje lahani yayinda kimanin mutane dubu dari kuma suka rasa wutar lantarki. Gwamnatin jihar tace an bude wuraren tsugunar da wadanda gidajensu suka lalace.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG